Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Yayi rantsuwar ne a gaban dubban magoya baya da suka taru a Filin Wasa na Heroes da ke Lusaka babban birnin kasar.
Yayin jawabin da ya yi jim kadan bayan rantsar da shi, sabon shugaban kasar, ya sha alwashin farfado da tattalin kasar, da kuma tabbatar da yancin walwala ga kowa da kowa.
Dan shekaru 59, wanda ya yi takara har sau shida a matsayin madugun ‘yan adawa na kasar, M. Hichilema, ya lashe zaben shugabncin kasar na ranar 12 ga watan Agusta, inda ya kada shugaban kasar mai barin gado, Edgar Lungu, da tazara ta kuri’u kimanin miliyan daya.
342/